07/09/2021
Waye Professor, Kuma yaya ake zama Professor din ?
-------------------------------------------------
Professor ko Professorship wani matsayi ne wanda ake bada shi a Jami'a dama wasu Cibiyoyin ilimi a mafi yawan Kasashen duniya.
Kalmar Professor an samo ta ne daga yaren French (Professeur) da kuma Latin Word, wacce kalmar take nufin mutumin da yake Kwararre a wani bangare na ilimi.
Yaya ake zama Professor ?
Zama Professor ba karamin aiki bane kuma ba na Rago bane na masu aiki ne tukuru, duk da wasu suna zargin cewa yanzu an siyasantar da harkar, wai indai kanada wani ubangida a siyasa to shikenan kawai zasu sa a baka, to alal hakika wannan zargi ne mara tushe bare mak**a, zaku fahimci hakane idan muka kawo bayanin sharuda da ka'idojin zama farfesa din. Shiyasa ku lura duk wanda aka cemaku Farfesa ne to ya wuce da sanin ka, dan duk inda kake tunane to tintini ya wuce gun, sai kuwa idan dan uwan sa ne Farfesa to wannan kuma Baba da Baba ne kai sai kaja gefe kasha Kallo.
Akwai ka'idojin zama farfesa a Jami'o'in Nigeria k**ar haka:-
1-Digiri na Uku (Ph.D/Dr.)
Dole sai kanada Degree na uku sannan ne ka samu dama ta farko ta zama Farfesa. Sannan dole sai kayi digirin nan na uku a Jami'ar da ta samu amincewa daga hukumar NUC, in kuwa ba haka ba to kai da wanda baiyi ba duk daya kuke.
2-Sannan sai kanada abinda suke kira da Area of Specialization (wato bangaren da kakeso ka kware a kansa)
Dan haka kai mai son zama farfesa dole tun yanzu kasan a wanne bangare ne kakeso ka zama Farfesa din dan ka zama cikin shiri da mayar da hankali kafin lokacin yazo.
3-Teaching experience
Amma wanda ake nufi anan shine wanda kayi a makarantun gaba da sakandare (Dan ka shekara 20 ko 30 kana koyarwa a Primary ko secondary to babu ruwan su dashi)
Sannan A kalla ka samu shekara Uku kana koyarwa da bincike da aikin al'umma a matakan nan guda hudu na koyarwa a Jami'a, gasu k**ar haka:
(a) Lacturer ii
Ka shekara uku kana Bincike da koyarwa da sauran su.
(b) Lacturer i
Shima haka, shekara uku
(c) Senior Lacturer
Shima shekara Uku
(d) Associate Professor
Shima shekara uku
Gaba daya shekara 12 kenan idan ka hada.
4-Assesment Scholarship.
Shine yafi muhimmanci kuma Jami'o'i s**a fi kulawa da damuwa da mayar da hankali a kan shi, ga duk wanda yakeso ya zama Professor.
Wannan Assesment din ya kunshi dubawa da auna ayyukan da ka wallafa a bangaren da kakeso ka zama Professor din.
Dan haka akalla ana bukatar ka wallafa ayyukan da basu gaza 60 ba kuma internationally, sannan a kalla acikin wadanda zasuyi assesing dinka a sami mutum daya daga wata babbar Jami'ar da ba ta Nigeria ba, k**ar America ko England, misali.
5-Sannan za'a yimaka Oral Interview
To daga nan idan ka samu adadin maki mafi karanci wanda jami'ar ta sanya dan bada wannan matsayi na Professor sai a tura da Sunan ka a University Council domin a nada ka Professor din (Wato Shaihu)
Saboda haka daga lokacin da aka nada ka farfesa dinnan to maganar ka indai akan ilimi ne to ta zama Hujja a cikin karatun boko (Dalibi zai iya kafa hujja da maganar ka)
Duk da dai akwai dan bambanci tsakanin Jami'o'i wajan bada Professorship din amma ba wani mai yawa bane